Kakakin Majalisar Dokokin Iran dinnan mai matukar tasiri, Ali Larijani, yau Lahadi ya ce muddun manyan kasashen Turai, ‘saboda kowani irin wani dalili,’ su ka kama tafarkin rashin adalci don su kawo wata gardama kan batun tsarin ‘yarjajjeniyar nukiliyar nan da aka kafa shekaru hudu da su ka gabata, wadda ta fara tangal-tangal tun bayan da Amurka ya fice daga ciki a 2018, to Iran fa za ta daina bayar da hadin kai ga hukumar sa ido kan makaman nukiliya (IAEA a takaice).
“Abin da kasashe uku na Turai su ka yi game batun nukiyar Iran … abin takaici ne,” a cewar Kakakin Majalisar Iran Ali Larijani, wanda ya taba kasancewa wakilin Iran a tattaunawar nukiliyar, kamar yadda gidan talabijin din gwamnatin Iran ya yada.
A makon jiya Kasashen Jamus, Burtaniya da Faransa sun ba da sanarwar gabatar da koke gaban kwamitin duba takaddamar aiwatar da yarjajjeniyar, wanda dama shi ne ya tanaji takaita shirin nukiliyar Iran, a madadin dage ma ta takunkumin da aka kakaba ma ta.