KAGARA: Gwamnatin Jihar Naija Ta Bayyana Sunayen Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su

Makarantar Sakandare ta Kagara.

Gwamnatin jihar Naija ta fitar da sunayen dalibai da malaman kwalejin kimiyya ta gwamnati da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Bayanai na nuni da cewa, ‘yan bindigan sun yi garkuwa da daliban kwalejin 27, da malamai uku, da kuma wadansu ma’aikata biyu da iyalansu 9, da ke zama a gidajen malamai da ke cikin makarantar.

An yayata wani hoton bidiyo da ake kyautata zaton maharan ne suka dauka, inda aka nuna mata da kananan yara, wadansu yara na kuka suna rokon gwamnati ta taimaka ta biya kudin fansan da maharan suka nema domin ceton rayukansu.

daliban-kagara-da-suka-kubuta-sun-bayyana-halin-da-suka-sami-kansu

dakarun-najeriya-sun-fara-farautar-yan-bindigan-da-suka-sace-daruruwan-dalibai-a-jihar-neja

majalisar-dattawa-ta-bukaci-buhari-ya-kafa-dokar-ta-baci-a-fannin-ilimi

Ministan watsa labarai Lai Mohammed, ya fada ranar Talata a wata ganawa da gwamnan jihar Naija Sani Bello ya yi da jami’an gwamnatin tarayya ranar Talata cewa, gwamnatin tarayya ta ta dauki matakin ganin an dawo da wadanda ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su lafiya. Ya kuma ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa, gwamnati ba za ta mika wuya ga masu aikata miyagun laifuka ba. Zata kuma dauki matakan da suka kamata na kare al’umma.

Yanzu haka dai hankali ya karkata kan maganar da Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya yi, cewa ‘yan Najeriya su yi damarar kare kansu daga mahara, batun da mutane da dama suka kushe a shafukan sada zumunta.

Karin bayani akan: Kagara, jihar Neja, Jihar Naija, Sani Belo, Nigeria, da Najeriya.