Gwamnatin jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya, ta ce za ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki kisan da aka yi a kananan hukumomin Kajuru da Kachia.
Gwamna Malam Nasiru El Rufa’i ne ya bayyana hakan, yayin wata ziyarar jaje da ya kai ga wadanda suka tsira daga harin, wanda aka kai a makon da ya gabata a yankunan biyu.
A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun mai bai wa gwamnan shawara kan harkar yada labarai, Samuel Aruwan, Gwamna El rufa’i ya kai ziyarar a yankin ne tare da wata tawaga da ta hada har da manyan jami’an tsaro a Karamai.
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnan ya bayyana cewa, tattara bayanai kan rikicin, na daga cikin hanyoyin da za a iya samar da dawwamamman zaman lafiya a yankunan.
Tawagar har ila yau ta kai ziyara inda aka binne 15 daga cikin mutum 40 da aka kashe a hare-haren.
Gwamna na El Rufa’i ya yi Allah wadai da hare-haren, inda ya kwatanta wadanda suka kai su a matsayin “marasa Imani.”