Kabilun tsaunin Mambila biyar ne suka taru a filin wasan garin Gembu domin rigakafin hana sake barkewar duk wani rikici da sunan kabilanci ko addini ko kiyayyar manoma da makiyaya.
An gudanar da taron ne a karkashin wata kungiya mai wanzar da zaman lafiya.
Shugaban kwamitin karamar hukumar, Pastor Godwin Sawa ya ce fitinar da ta faru kwanakin baya inda aka samu hasarar rayuka da dauruwan shanu ba ta addini ba ce kuma an dauki duk matakan hana aukuwar irinta nan gaba.
Ya ce damuwar daya ce, ita ce damuwar manomi da makiyayi. Manomi yana son wurin noma haka ma makiyayi na bukatar wurin da zai yi kiwon dabbobinsa. Abun da ke hada fada ke nan.
Babban jami’in ‘yansanda na yankin Sardauna, Alabura Dangi, ya ce kabilun sun zama daya domin dukansu suna fulatanci.
A taron, Fulani makiyaya sun bukaci a hukumta baragurbin dake tsakaninsu da suke da hannu a kashe-kashen da suka gudana tare da biyan diya ga wadanda suka rasa shanunsu.
Shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya, Injiniya Zakari Ahmed Guroji, ya karfafa dawo da martabar sarakuna a matsayin wata hanyar hana irin fitinar da ta taso.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5