Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp, ya tsawaita kwantirakinsa a kungiyar.
Klopp wanda ya koma kungiyar ta Liverpool a watan Oktoban shekarar 2015, a yanzu haka ya sake rattaba hanu zuwa shekarar 2024.
Ya taimaka wajan farfado da darajar kungiyar, inda ta lashe kofin Zakarun Turai UEFA Champions League na 2018/19, ta kuma kammala a matsayi na biyu cikin gasar Firimiya lig na Ingila.
Bayan haka kuma a gasar zakaru na bana ta samu zuwa wasannin zagayen gaba na kungiyoyi 16 domin ganin ta kare kambunta.
A bana kungiyar ita ke saman teburin gasar na Firimiya da tazarar maki 8 tsakaninta da Leicester City, da take binta inda take yunkurin kawo karshen shekaru 29 da tayi rabonta da kofin.
Kocin mai shekaru 52, da haihuwa ya bayyana jin dadin zamarsa a kungiyar ta Liverpool, inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunci na yanar gizo cewar baya tunanin barin kulob din.
A ranar Asabar mai zuwa Liverpool zata karbi bakonci Watford a wasan mako na 16 cikin gasar Firimiya lig na bana.