Madugun ‘yan adawar kasar Venezuela, Juan Guaido, na yin kira ga kasashen duniya da su goyi bayan kokarin da yake na hambarar da gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro wanda matsalolin siyasa suka dabaibaye, a kuma maido da tsarin dimokaradiyya a kasar dake yankin nahiyar Amurka ta Kudu.
Guaido, shugaban ‘yan adawar dake da rinjaye a Majalisar dokokin kasar, ya ayyana kansa a matsayin shugaban rikon kwarya a makon da ya wuce, bayan da Majalisar dokokin kasar ta ayyana cewa, sake zaben Maduro da aka yi a watan Mayun shekarar da wuce ba a yi shi bisa ka'ida ba, yayinda wasu da yawa suka yi watsi da neman takara wasu kuma aka hana su tsayawa takarar. Amurka ta amince da Guaido, a matsayin shugaban kasar mai rikon kwarya.
A wani ra’ayi da aka rubuta yau Alhamis a jaridar The New York Times, Guaido ya ce fiye da kasashe 50, ko dai suka yarda da shi a matsayin shugaban rikon kwarya ko kuma suka yarda da majalisar dokokin kasar a matsayin hukuma mafi karfi a Venezuela, kuma ya yi kira ga Babban Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, akan a taimaka wa kasar da agajin jinkai. Ya kuma ce ya fara nada jakadu da gano, tare da maido da dukiyoyin kasar da aka boye a kasashen waje.
Biyo bayan ayyana kan sa a matsayin shugaban rikon kwarya da yayi a makon da ya gabata, Guaido na neman taimakon kasashen duniya, ciki har da majalisar dinkin duniya.
WASHINGTON D.C. —