JTF Ta Gabatar Da Matasan Da Ake Zargi Da Kisan Janar Shuwa

Major General Lawrence Ngubani, shugaban Kwamitin Bincike na Ma'aikatar Tsaron Najeriya dangane da Baga a lokacin da yake tattaunawa akan binciken da suke gudanarwa.

Tun 11 ga watan Decembar shekara ta 2012, wasu ‘yan bindiga suka bindige Janar Shuwa a gidansa dake anguwar Goge dake tsakiyar Maiduguri.

Wannan lamari dai ya baiwa mutane al-ajabi ganin yadda gidan Janar din ke zagaye da Sojoji. Amma har sai da ‘yan bindiga suka samu daman ratsawa, kuma suka harbe shi.

A yammacin Litinin ne, kakakin rundunar JTF, Laftanal Kanal Sagir Musa ya gabatar wa da manema labarai wasu matasa uku da ake zargi da aikata wannan mummunan laifi.
Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu ya samu daman tattaunawa da wadannan matasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Mutanen Da Ake Zargi Da Kashe Janar Shuwa


A wata sabuwa kuma, wasu rahotanni na cewa an ji karar bindigogi da boma-bomai na tashi a cikin garin Bama dake jihar Borno, kuma mutanen garin na cikin wani hali, suna arcewa zuwa cikin daji.