Jonathan Ya Isa Laberiya Don Sa Ido Kan Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu

Tsohon Shugaban kasa, Jonathan Goodluck

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck E. Jonathan ya sanar a shafin X cewa ya isa birnin Monrovia na kasar Laberiya tare da tawagar dattawan Afirka ta Yamma da ake kira WAEF a takaice.

Jonathan ya kai ziyarar ne don shirye shiryen zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar Talata 14 ga watan Nuwamba a wannan shekarar ta 2023 a cewar jaridar News.ng

Jonathan ya samu rakiyar tsohon Firai Ministan Burkina Faso kuma tsohon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, Kadre Ouedraogo, da kuma ma'aikatan sakatariyar WAEF.

A cikin sakonsa na twitter, shugaba Jonathan ya yi wa al'umar kasar Laberiya fatan alheri, ya kuma bayyana fatansa na ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ya kuma yi kira ga ‘yan takarar shugaban kasar biyu da mabiyansu da su yi aiki da yarjejeniyar Farmington River Pact don tabbatar da cewa Laberiya ta ci gaba da samun zaman lafiya a lokacin zaben zagaye na biyu da kuma bayansa.

“A matsayinsa na wakilin kungiyar dattawan Afirka ta Yamma, Jonathan zai kasance cikin masu sa ido na kasa da kasa kan yadda zaben ke gudana domin tabbatar da gaskiya da adalci," a cewar tawagar a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa, "Kasancewarsa a Monrovia na nuna muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa da sa ido wajen inganta tsarin dimokradiyya a fadin nahiyar."

Kungiyar dattawan Afirka ta Yamma, kungiya ce da ke hada fitattun mutane daga yankin yammacin Afirka don ba da jagoranci da goyon baya ga zaman lafiyar siyasa, ci gaban tattalin arziki, da zaman lafiya a yankin baki daya.