Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP ya ci zaben jihar Nasarawa. Da ya ke bayyana sakamakon zaben, babban jami’in bayyana sakamakon zabe na jihar ta Nasarawa Furfesa Abdulmumini Hassan Rafin Dadi, ya bayyana cewa Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sami kuri’u dubu dari biyu da saba’in da uku da dari hudu da sittin, yayin da kuma shi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari (murabus) ya samu kuri’u dubu dari biyu da talatin da shida da dari takwas da talatin da takwas .
A zaben Majalisar Dattawa kuwa, Salihu Hussaini Agebola na Jam’iyyar APC ne ya doke Suleiman Adokwe na jam’iyyar PDP a Nasarawa ta Kudu; a Nasarawa ta Tsakiya kuma, Sanata Abdullahi Adamu na jam’iyyar APC ne ya doke Sanata Aliyu Wadada na jam’iyyar PDP; sannan a Nasarawa ta arewa kuwa Aruwa gwinka na jam’iyyar PDP ne ya ci zaben.
A jihar Filato kuwa, jami’in hulda da jama’a na hukumar zabe Usuratin Imahiyebo, ya shaida ma wakiliyarmu Zainab Babaji da misalign karfe daya na rana cewa, sun samu sakamako daga kananan hukumomi 12; sun a jiran sakamako daga kananan hukumomi biyar kafin su bayyana cikakken sakamakon .
Your browser doesn’t support HTML5