Mukarraban Buhari Sune Suke Tsare Da Sambo Dasuki-Sarki Jokolo

Shugaba Buhari da wasu mukarrabansa a taron APC

Sarkin Gwandu na 19, yace ba ya tsammanin shugaba Muhammadu Buhari yana da hannu a ci gaba da tsare Kanar Sambo Dasuki mai ritaya.

Alhaji Mustapha Haruna Jokolo, wanda yake magana dangane da sabon littafi kan tarihin rayuwar Sarkin Gwandu na 20 Alhaji Muhammadu Bashar Ma'aji Jega, littafin da yayi magana kan yadda aka shirya juyin mulkin da tsohon shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi na kifar da gwamnatin Janar Buhari, yace da farko dai babu wani abu cikin littafin banda karai-rayi.

Gameda tsohon mai baiwa shugaba Jonathan shawara kan harkokin tsaro,kanal Sambo Dasuki mai ritaya, wanda yanzu kusan shekaru uku yana tsare, kan zargin almundahana da kudade da aka ware don yaki da Boko Haram, Sarki Mustapha Haruna Jokolo, yace a iya saninsa Sambo Dasuki ba barawo bane. Saboda idan dukiya yake nema, ya rike mukamai a baya wadanda da dukiya yake nema da ya tara ta.

Sarki Mustapha Jokolo, yace a tsammaninsa shugaba Buhari bashi da hanu a ci gaba da tsare Sambo Dasuki, domin ya taba yiwa shugaban magana kan batun Sambon, kuma shugaba Buhari ya ce a tafi a zauna a tattauna da Sambon. Domin haka, yana ji dai wasu daga cikin mukarraban shugaba Buhari sune suke da matsala da Sambo Dasuki.

Ga Karin bayani da tsohon sarkin yayi.