Jama'ar Jihar Kano Sun Yi Mamakin Dage Zabukan Najeriya

Kasuwanni da cibiyoyin hada-hadar cinikayya a birnin Kano da kewaye na ci gaba da zama a kulle yayin da kungiyoyin sanya ido akan zabe da kuma 'yan takara ke ci gaba da bayyana furuci dabam dabam akan wannan matakin na hukumar INEC.

Zirga zirgar Jama'a a sassan birnin Kano ta ragu sosai, lamarin da ya sanya galibin tituna a birnin da kewayen sa suka kasance babu ababen hawa sosai. Hatta masu kananan sana'o'in hannu na ci gaba da zama a gida.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da 'yan siyasa, musamman wadanda suka tsaya takarar zabe ke bayyana alhinin su game da wannan mataki na hukumar zaben Najeriya.

Hajiya Hauwa Ibrahim El-Yakub, dake takarar kujerar majalisar dattawan Najeriya daga mazabar Kano ta tsakiya a karkashin inuwar Jam'iyyar NPM ta bayyana cewa ba su ji dadin wannan matakin ba kuma wannan na nuna rauni a bangaren gwamnati. Ta kuma kara da jan hankalin hukumar zabe akan ta tabbata an gudanar da zabe ranar Asabar mai zuwa.

A nasu bangaren kungiyoyin sanya ido akan wannan zabe na bayyana mamaki akan wannan hukunci na hukumar zaben Najeriya na dage zaben, Comrade Abdulrazaq Alkali, shine daraktan daya daga cikin kungiyoyin da hukumar zabe ta amincewa su sanya ido akan wannan zaben, kungiyar da ake yiwa lakabi da org for community civic engagement da turanci. Ya ce dalilan da hukumar zaben ta bayar basu isa su sa a daga zabe ba. Bayan haka, ya kuma nuna damuwar sa akan kare kayan zaben da aka riga aka tura wurare dabam dabam daga nan zuwa sati mai zuwa.

Haka zalika, Comrade Alkali ya shawarci hukumar zabe dangane da bukatar ofishin Atoni Janar na kasa game da 'yan takarar Jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

Ya kuma ja hankalin hukumar zaben akan kaucewa duk wani abu da zai sa a yi zargin wata jam’iyya na amfani da ita.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Jama'ar Jihar Kano Sun Yi Mamakin Dage Zabukan Najeriya - 3'34"