Jiya Sojojin Iraqi Sun Kwace Birnin Kirkuk daga Hannun Mayakan Kurdawa

Dakarun Iraqi suna shiga birnin Kirkuk

Tun daga ranar da kurdawa suka ce sun balle daga kasar Iraqi aka san ba zasu kwashe lafiya ba saboda dakarun Iraqi da Amurka ta horas basu yi wata wata ba suka farma kurdawan kana jiya suka kwace Kirkuk, birnin dake da dimbin albarkar man fetur

A Jiya Litinin sojojin gwamnatin Iraqi suka kutsa birnin Kirkuk dake hannun mayakan Kurdawa, suka kame muhimman wurare da suka hada da ofishin gwamna da sansanonin soja da kuma wani fegi na man fetur.

Cikin gaggawa sojojin Iraqi wadanda sojojin Amurka suka horas, suka shiga birnin dake a Arewacin kasar, a bias umurnin Fara Minista Haider al-Abadi, suka kuma ‘daga tutar Iraqi a wuraren da tutocin Kurdawa suke.

Wannan abu dai ya zo ne kasa da kwana guda bayan kaddamar da wani aikin mayar da martani kan kuri’ar da Kurdawa suka kada watan da ya gabata ta neman ‘yanci wanda gwamnatin tarayya ta ayyana a matsayin baya bisa doka.

Gwamnatin Iraqi dai ta bayyana karbo ikon birnin da cewa ba a fuskanci wani kalubale ba, amma wata kungiyar agaji ta ce an kashe wasu sojojin Kurdawa na Peshmerga da sojojin Iraq a fadan da aka yi cikin dare a Kudancin birnin Kirkuk kafin sojojin gwamnatin su sami damar shiga birnin.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, wadda ke goyon bayan sojojin Iraqi, wadda kuma ta taimaka wajen horas da sojojin Kurdawa a yakin da akayi da kungiyar IS, ta ce sojojin Iraqi sun hada kai da maykan Peshmerga don fatattakar na Kurdawan..