: Jiya Lahadi wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 13 a birnin Maiduguri na arewa maso gabashin Najeriya mai fama da tashe-tashen hankula
Harin, wanda aka kai da yammacin jiya Lahadi, ya kuma raunata wasu mutane 5. Wasu hare-hare biyu kuma da su ka biyo baya, sun raunata mutane sama da 12.
Kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane sama da 20,000 a tsawon shekaru 8 da ta yi ta na tayar da kayar baya ga gwamtain Najeriya, a yinkurinta na kafa tsattsaurar daular Islama a yankin arewa mai rinjayen Musulmi. Maiduguri, babban birnin jahar Borno, shi ne akidar ta Boko haram.
Kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce tashe-tashen hankulan Boko Haram sun jefa miliyoyin farar hula a yankin na Tabkin Cadi cikin yanayi na matukar bukata. Mutane kimanin milyan 2.3 ne aka raba su da muhallansu a Najeriya, da Kamaru da Cadi da kuma Janhuriyar Nijar, kuma wasu mutanen sama da miliyan 7 na fuskantar karancin abinci.