Jiya Lahadi Firayim Ministan Ukraine ya ce zai yi murabus gobe Talata

Firayim Ministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk

A jiya Lahadi Firayim Ministan Ukraine da ake ta faman artabu maida shi Arseniy Yatsenyuk yace zai yi murabus don bada damar kafa sabuwar gwamanti domin kawo karshen rudanin siyasar birnin Kyiv da ta ki ci ta ki cinyewa. Firayim Ministan ya fada a kafar talbijin da kuma shafinsa na abota na Twitter.

Inda ya kara da cewa zuwa ranar Talata idan Allah ya kaimu zai mika takardar tasa ta murabus gaban majalisar dokokin kasar. Ya bayyana cewa, kawai an cinno wutar rikicin siyasar kasar ne da gangan don ganin ya sauka. Tare da nuna yadda wannan rudani ya makantar da ‘yan siyasar kasar har suka kasa kawo canji a kasar.

A jiya Lahadi ne mataimakin shugaban Amurka Joe Biden bai yi kasa a gwiwa wajen kiran Mista Yatsenyuk ta wayar tarho bay a kuma taya shi murnar wannan mataki da ya dauka ba, wanda yace wannan abun bukata ne a Ukraine don shawo kan matsalolin da ke addabarta a siyasance da kuma na tattalin arzikinta.