Jiya Aka Bude Taron Manyan Hafsoshin Soja Na Kasashen Afirka Da Amurka A Abuja

Manyan Hafsan sojojin Najeriya da na Amurka

Taron manyan hafsoshin sojojin Afirka da na Amurka taro ne na gano bakin zaren warware matsalolin tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta domin kawar da zaman dar dar a duniya

An yi kira ga kasashen duniya, musamman ma hukumomin tsaro da jami'an su su hada kai domin samun gajiyar tsaro.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin mukaddashin babban hafsan hafsoshin sojojin Amurka Janar James McConville shine yayi wannan kira a jawabin da yayi a taron manyan hafsoshin soja na Afirka da na Amurka, inda ya bayyana makasudin taron da dangantakar dake akwai tsakanin kasashen Afirka da Amurka.

Janar McConville ya yi magana akan mahimmancin yin aiki tare domin cin moriyar tsaro a Afirka da hakan ka iya taimakawa duniya baki daya a cewarsa. Ya kara da cewa dakarun Amurka na jin dadi da irin atisayin da su keyi da dakarun Afirka domin fuskantar kalubalen tsaro.

Shi ko a cikin jawabinsa babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Abayomi Gabriel Olanishakin, ya bayyana irin matasalolin tsaro da Afirka ke fuskanta a halin yanzu. Ya ce akwai tada kayar baya da garkuwa da mutane da fashi da makami da tsatsaurar ra'ayi da yaduwar kananan makamai da fashi akan teku. Duk wadannan abubuwa ke haddasa matsalar tsaro a nahiyar Afirka yayinda duniya baki daya ke zaman dar dar.

Inji Janar Olanishakin akwai bukatar lalubo wasu sabbin hanyoyin da za'a bi a tunkari matsalolin da ya lissafa.

Babban Hafsan Hafsoshin Nijar Janar Sadiku ya bayyana ra'ayinsa akan taron. Ya gayawa wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina cewa, suna jin dadin taron tare da sauran hafsoshin kasashen Afirka da na Amurka. Ya yi fatan su kare taron lafiya.

Kazalika shi ma hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi karin bayani akan mahimmancin taron. Hadin kan rundunonin Afirka shi ne abun dake kan gaba, domin su bayyana abubuwan dake damun su ta fannin tsaro domin su tattaunasu da takwarortin su na Amurka.

Ga Hassan Maina Kaina da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Jiya Aka Bude Taron Manyan Hafsan Sojojin Kasashen Afirka Da Na Amurka A Abuja - 2' 23"