Jirgin Yakin Najeriya Ya Yi Hatsari a Borno

Wani jirgin yakin Najeriya mai suna Mi-35P combat helicopter

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya tabbatar da aukuwar hatsarin a shafinsu na Twitter, inda ya ce ana gudanar da bincike kan abin da ya haddasa hatsarin.

Rahotanni daga Najeriya na cewa wani jirgin sama mallakar sojojin kasar ya fadi a yankin Damasak da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya tabbatar da aukuwar hatsarin a shafinsu na Twitter, inda ya ce ana gudanar da bincike kan abin da ya haddasa hatsarin.

“Wani jirgin saman sojin Najeriya ya yi hatsari yayin da yake taimakawa runduna ta 145 a fagen yaki a Damasak da ke arewacin jihar Borno.” In ji sanarwar da Daramola ya wallafa shafin Twitter.

Ya kuma kara da cewa, “hatsarin ya faru ne da misalin karfe 7:45 na yammacin ranar Talata 2 ga watan Janairun 2019, amma har yanzu ba a samu cikakkun bayanai kan abin da ya haddasa hatsarin ba.”

“Da zaran mun samu cikakkun bayanai za mu bayyanawa jama’a.”

Wannan hatsari ya faru ne yayin da dakarun na Najeriya ke yakar mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.