Hukumomi a wani lardi na gabashin Afghanistan sun ce jirgin sama mara matuki na Amurka ya kai hari akan wata kungiya da ake zaton gungun mayakan ISIS ne, inda akalla mutane 18 suka mutu, ciki har da farar hula.
Kwamandan rundunar ‘yan sanda Mohammad Ali ya fadawa Muryar Amurka yau Laraba cewa wasu da ba mayakan sa-kai bane da yawa na cikin wadanda suka jikkata a harin da aka kai a gundumar Achin na lardin Nangarhar, wanda ya hada iyaka da Pakistan.
Dan sandan yace manyan kwamandojin kungiyar ta Daesh guda 2 na cikin wadanda harin ya shafa.
Wani mai magana da yawun rundunar sojan Amurka, brigadier Janar Charles Cleveland, ya tabbatarwa muryar Amurka cewa dakarun Amurka sun kai hari ta sama a yankin yau Laraba. Amma bai bada karin bayani ba saboda dalilin tsaro.