Jiran Aikin Ofis Ko Jiran Kare A Karofi - Hauwa Aadamu

Hauwa Adamu Kiyawa matashiya wacce ta ce ta fara sana’ar sayar da cupcakes wato kayan tande-tande dangogin fulawa domin zamo mai dogaro da kai, a lokacin bukukuwan sallah karama na bana.

Ta ce tun tana makarantar jami’a ne ta fara sana’ar cupcakes, inda take sayarwa ‘yan uwanta dalibai a cewar ta wata hanya ce ta rage zama tare da samar da wasu kudade a hannunta bayan an fito daga makaranta ko a lokatan da ba’a darasi.

Matashiyar ta ce a yanzu ya zama dole ne ga matasa su zamo masu dogaro da kai ba sai an jira aikin ofis ba a wannan lokaci na matsin rayuwa, ta kara da cewa tun matashi na dalibi ya kamata ya zamo mai dogora da kai.

Hauwa ta ce tana tallata hajarta ne ta kafar sadarwa ta instrgram ko shafin whatsApp da sauransu kuma a yanzu duk mai bukata da zarar ya ayyana bukatar sa zata yi masa mussamam idan aka bukaci ta yi kwana guda kafin ranar.

Your browser doesn’t support HTML5

Jiran Aikin Ofis Ko Jiran Kare A Karofi - Hauwa Aadamu