Mr. Cavusoglu yace nan bada jumawa ba kasarsa da Amurka zasu fara gagarumin fada da 'yan kungiyar ISIS, da zai kai ga samar da yanayi da ya dace ga 'yan tawayen Syria masu sassaucin ra'ayi wadanda suke fafatawa da 'yan bindigar.
Ministan harkokin wajen yayi magana a lokacin ziyarar da yake yi a Malaysia, inda ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka John kerry a gefen taron kolin na yanki.
A cikin watan jiya ne Turkiyya ta amince da girke dakarun Amurka a wani sansanin mayakan samanta dake gari da ake kira Incirlik kusa da kan iyakarta da Syria daga kudancin kasar.
Jami'ai sun bayyana shirin a zaman wani kokari na kjirkiro da ani yankin da "babu 'yan ISIS", mai fadin kilomita 100 a arewacin Syria.