Karin kai farmaki da jiragen saman yaki da Amirka ta kara kaimun sun ka iya zama fara yunkurin murkushe kungiyar a IS a yayinda take kokarin ganin yankin Arewacin Afrika, bai fita daga hannun ta ba..
WASHINGTON DC —
Rundunar hadin guiwan Amurka da Afrika ta bada sanarwar sabbin hare hare takwas akan IS jiya Talata a birnin Sirte dake gabar teku da ke zama sansanin gudanar da aiyukan kungiyar ta yan ta’addan .
Ga baki daya Amurka ta kai harin jiragen sama 28 akan IS azaman wani bangare na shiri da ta kira Operation Odyssey Lightning wanda ta fara a ranar daya ga watan Augusta biyo bayan bukata da gwamnati Lybia tayi a wata yarjejeniya.
Wani jami’in Amurka da ya zanta da VOA da bai so a bayyana sunansa ba yace rundunar Amurka na musamman suna ayyukansu a wurin ta jami’ina da bai yi Karin bayani akansa ba