A cewarsa goyon bayan da aka nuna masa kan fafutukar kafa dimokradiyaya da yake yi, hanya ce madaidaiciya.
Dan shekara 71, lai ya kasance daya daga cikin mutum 10 da aka kama a ranar Litinin kan zargin sun keta dokar tsaro da China ta ayyana a ranar day aga watan Yuli.
Daga cikin mutum goman har da ‘ya’yansa biyu, da wasu manyan jami’an kamfaninsa hudu sannan sai wasu masu fafutuka uku da aka kama, ciki har da Agnes Chow mai shekara 23.
Kafafen yada labaran cikin gida sun ce bayan da aka saki Lai akan beli an rufe kadarorins da kudinsu ya kai dala miliyan shida da rabi.
Bayan da aka kama shi, gwamnatin ofishin harkokin China da ke Hong Kong, ta zargi Lai da gidan jaridarsa da laifin haddasa zanga zanga a yankin na Hong Kong, inda suka ce ya yi amfani da kafar wajen yada jita-jita da ta da tarzoma