Jimillar Mutuwa Ta Kai 30 A Mogadishu, Bayan Fashewar Bama-Bamai

Mahukunta a kasar Somalia sun ce, yawan mutanen da su ka mutu sanadiyyar tagwayen hare-haren bam a kusa da Fadar Shugaban kasa da ke Mogadishu babban birnin kasar, ya haura zuwa 30.

Daraktan sashin hulda da jama'a na hukumar yankin Benadir Mukhtar Dhaga, ya ce wasu mutane 54 sun jikkata.

Fashewa ta farko a ranar ta Asabar, ta auna wani wurin duba ababen hawa ne da ke kusa da ginin wasanni na kasa, da kuma mashiga ta baya ta fadar Shugaban kasa. Fashewa ta biyu kuma, ta auku a kusa da ta farkon. Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin wannan harin.

A cikin wadanda suka mutu a fashewar bam din na farko, harda wani fitaccen dan jaridar Somalia, Awil Dahir Salad, wanda ya ke aiki da wani gidan talabijin na Landon, a matsayin mai gabatar da wani shiri mai suna “Dood Wadaag”