Jihohin Washington da Minnesota sun kalubalnci dokar hana yan wasu kasashe zuwa nan Amirka

HOTUNA: Kungiyoyin Dalibai Daban Daban Sun Sami Halartar Zanga Zangar Mata Domin Bayyana Ra'ayoyinsu Kan Manufofin Gwamnatin Donald Trump

Alkalin wata kotun taraiyar a jihar Washington James Robart ya yanke hukuncin dakatar da haramtawa yan yawon bude ido da yan gudun hijira daga kasashe guda bakwai wadanda yawancin al’ummar su Musulmi ne, shigowa nan Amirka da aka kaddamar a makon jiya.

Tuni dama jami’an kwastan da dogarawan tsaron kan iyaka suka ce dukkan matafiya da suke da izinin shigowa nan Amirka za’a bari su shigo.

Fadar shugaban Amirka ta White House ta gabatar da sanarwar dake cewa ma’aikatar shari’ar zata gabatar da umarnin gaggawa akan wannan mataki.

Haka kuma sanarwar ta kare umarni ko kuma dokar shugaba da Donald Trump ya gabatar akan cewa bai karya doka ba.

A yayinda yake maida martini shugaba Trump yace Amirka zata shiga matsala idan ta kasa yanke shawara akan wanda zata bari ya shigo mata kasa

Jiya Juma’ a alkali James Robart ya yanke hukuncin cewa jihohin Washington da Minnesota bisa doka suna da yancin kalubalantar umarnin shugaba Donald Trump