Jihohin Da Za a Yi Gwagwagwa a Zaben Gwamna

Hotunan 'yan takara shugaban aksa da na gwamna a Najeriya

A yau al’umar Najeriya suke kada kuri’a a mafi aksarin jihohin kasar, domin zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.

Wannan zabe na da matukar muhimmanci ga ‘yan kasar, lura da cewa gwamnatoci a matakan jiha, su suka fi kusanci da jama’a.

Duk da cewa akwai zabukan ‘yan majalisun da za a yi, zaben gwamnoni shi ne aka fi kai ruwa rana akansa, inda da wuya ka ga wata jiha da ba ta da takaddama daya ko sama da haka, musamman tsakanin ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar kasar, wato APC mai mulki da PDP mai adawa.

Ko da yake, akan kuma samu takaddama tsakanin jam’iyya guda, kamar abin da ke faruwa a jihar Zamfara inda aka yi ta kai ruwa rana a jam’iyyar APC mai mulki, wacce har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ake ta takaddama kan dan takararta.

KANO

A Kano da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya, za a fafata ne tsakanin manyan jam’iyyun kasar, wato APC mai mulki, wacce dan takararta Abdullahi Umar Ganduje zai mata takara.

A gefe guda kuma, akwai dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa, wacce take fuskantar rikicin cikin gida tsakanin dan takarar da tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke marawa baya, Abba K. Yusuf da Alhaji Ibrahim Ali Amin.

Al Amin na ikrarin ba a bi ka’ida ba wajen zaben fidda gwanin da ya samar da Abba K. Yusuf a matsayin dan takara, lamarin da ya sa ya garzaya babbar kotun Kano, ya sa aka soke takarar Abba.

Amma a ranar Alhamis, kotun daukaka kara a jihar Kaduna ta jingine hukuncin kotun ta Kano, inda ta ce Abba ne dan takarar gwamnan a jam’iyyar ta PDP.

Ko da yake, bangaren su Al Amin sun ce za su kalubalanci hukuncin a kotun koli.

Masu fashin baki a fannin siyasa sun yi tsokacin cewa, wannan takaddama da ta dabaibaye PDP, za ta iya shafar kuri’un da za su samu.

Shi kuwa Gwamna Ganduje, wanda ke neman wa’adi na biyu, ya shiga zaben ne watanni kadan bayan wata badakalar cin hanci da rashawa da jaridar Daily Nigerian ta wallafa bidiyo akai, yana karban dubban daloli, zargin da ya musanta.

Tasirin da wannan badakala za ta yi a zaben na yau, abu ne da masana harkar siyasa suka ce sai an gani.

A bangare guda kuma, akwai dan takarar jam’iyyar PRP, Malam Sagir Takai, wanda shi ke da dumbin magoya baya a jihar ta Kano, wacce ke da adadin masu kada kuri'a da ya haura miliyan biyar.

KADUNA

A jihar Kaduna da ke makwabtaka da Kanon, takarar ta fi zafi ne tsakanin, Gwamna Nasiru El Rufa’i na jam’iyyar APC da kuma dan takarar PDP Isa Ashiru da ke adawa da shi.

Wasu na ganin, kayar da manyan ‘yan siyasa da Ashiru ya yi irinsu Sanata Suleiman Hunkuyi da tsohon shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa, wato NEMA, Muhammad Sidi a zaben fidda gwani, alama ce da ke nuna cewa Ashiru ba zai zamanto kanwar lasa ba.

Da yawa kuma na ganin El Rufa’i zai iya samun nasara cikin ruwan sanyi idan aka yi lakkari da yadda wasu ke ikrarin ya yi aiki a shekaru hudun da suka gabata.

ADAMAWA

Kamar dai sauran jihohin Najeriya, a yau ana fafatawa ne a tsakanin ‘yan takarar gwamna 29, da kuma na kujerar ‘yan majalisar dokokin jihar 25.

Sai dai fafatawar ta fi zafi ne a tsakanin dan takarar jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Sanata Muhammad Bindow Jibrilla da takwaransa Sanata Abdul'Aziz Murtala Nyako na jam'iyyar ADC da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ahmadu Umaru Fintiri na jam'iyar PDP, kana da tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Emmanuel Bello na jam'iyyar SDP.

Kamar yadda aka samu rarrabuwar kawuna a tsakanin jam’iyyar PDP a Kano, ita ma jam’iyyar APC a jihar ta Adamawa na fuskantar hakan, kan takaddamar da ta samo asali daga batun yin zaben “SAK” Ko kuma cacanta.

SOKOTO

A jihar Sokoto, karawar za ta fi zafi ne tsakanin Gwamna Umaru Tambuwal na jam’iyya mai mulki wato PDP da kuma tsohon mataimakin gwamna Ahmed Aliyu.

Aliyu shi ne mataimakin Tambuwal kafin shi Tambuwal ya sauya sheka zuwa PDP, yayin da shi kuma Ahmed Aliyu ya ci gaba da zama a APC har ta tsayar da shi dan takararta.

Sai dai wasu manazarta na ganin, fafatwar za ta yi zafi ne saboda ‘yan takarar biyu, dukkansu matasa ne, yayin da kuma sun yi aiki tare a baya.

Amma babban abu shi ne, a baya mabiyansu duk daya ne, lamarin da ake ganin zai iya kara zafafa takarar.

Amma wasu masu fashin baki na ganin cewa, lashe jihar da shugaba Buhari ya yi a zaben shugaban kasa da aka yi a watan Fabrairun da ya gabata, ‘yar manuniya ce cewa, Aliyu ka iya yi wa tsohon mai gidansa fintinkau a yawan kuri’u. Lokaci ne kawai zai nuna abin da zai faru.

PILATO

A jihar Pilato da ke tsakiyar arewacin Najeriya, akwai ‘yan takara da dama da ke neman kujerar gwamna, amma takarar za ta fi zafi ne tsakanin Gwamna mai ci Simon Lalong na jam’iyyar APC da kuma dan takarar jam'iyyar babbar adawa ta PDP, Lt. Gen. Jeremiah Useni (mai ritaya.)

Baya ga wadannan ‘yan takara, akwai wasu 19 da ke neman kujerar gwamnan daga jam’iyyun ADC, SDP, GPN da sauransu.

Gwamna Lalong ya fadawa Muryar Amurka cewa, “In Allah ya yarda nasara ta mu ce, ba wai muna tsaron zabe ba ne, muna so ne a yi zabe lafiya.”

Shi kuwa Gen. Useni, kalubalantar masu cewa shekarunsa sun ja ya yi.

“Su zo mu yi kokuwa, akwai shi Buhari ai ya fi ni shekaru, amma yana kula da jihohi 36.” Inji Useni.

IMO

Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, jiha ce da ke karkashin mulkin jam’iyyar APC.

Sai dai gwamnanta, Rochas Okorocha, wanda jam’iyyar ta dakatar a kwanan nan, bisa zargin yi wa jam’iyya zagon kasa, ya kammala wa’adinsa biyu, inda yanzu wanda zai gaje shi ne abin takaddama.

Amma ya samu nasarar lashe kujerar Sanata.

Masu lura da al’amura na ganin, rashin jituwa tsakanin dan takarar jam’iyyar APC, Hope Uzodinma da gwamna Okorocha ka iya kawo cikas ga nasarar APC a jihar.

Takaddamar ta samo asali ne saboda goyon baya da Okorocha ya ke bai wa surukinsa kuma dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar AA, Uche Nwosu.

Wannan dalili, kamar yadda rahotanni suka nuna, shi ya sa a kwanan nan jam’iyyar ta APC ta dakatar da Okorocha.

OGUN

Kamar jihar Imo, a Ogun da ke Kudu maso yammacin Najeriyar, gwamnan jihar Ibekunle Amosun, wanda shi ma jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta dakatar, ya nuna goyon baya ne ga wani dan takara da ba na jam’iyyarsa ba.

Tun bayan da mutumin da yake so ya gaje shi ya fadi a zaben fidda gwani a jam’iyyar ta APC, Amosun ya koma marawa Adekunle Akinlade baya, wanda yanzu haka yake takara karkashin jam’iyyar APM.

A bangaren babbar jam’iyyar adawa ta PDP, yayin da hukumar zabe ta INEC ta amince cewa Buruji Kashamu ne dan takarar gwamna na PDP, ita kuwa jam’iyyar, ta nace sai Oladipo Adebutu.

Kamar dai yadda masu iya magana ke cewa, yau ne za a yi ta kare, inda nan da wasu 'yan kwanaki ne kowa zai san matsayarsa.