Wannan matsala ta jawo kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya da ta sake duba harkar sayar da hannun jarin wutar lantarki da aka yi a kasar.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Legas, Enugu, Kaduna, Abia, Anambra, Ebonyi, Imo da kuma Birnin Tarayya Abuja.
Tabbacin rugujewar cibiyar wuta ta kasa ya bayyana ne a wata takarda mai dauke da sa hannun kampanin wuta ta Legas ga dukan wadanda ke sayan wuta ta hannunsu, cewa an samu matsala a cibiyar wutar lantarki ta kasa kuma ta shafi wadannan Jihohin.
Shugaban Kungiyar Kare Hakkin Masu Amfani da wutar lantarki a Najeriya wato Consumer Protection Network Initiative a turanci, Kola Olubiyo ya ce wannan hali na rashin wuta ya sa kungiyarsa ta aike wa shugaba Muhammadu Buhari takarda ta musamman.
Amma mai ba Shugaban Kasa Shawara a harkar Manyan ayyuka, Ahmed Zakari, ya ce gwamnati tana aiki tukuru wajen magance matsalar.
Abin jira a gani shi ne irin matakin da mahukunta za su dauka domin biya wa masu amfani da wutar latarki bukatunsu na yau da kullum.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5