Jihar Taraba Ta Bankado Ma'akatan Bogi

Ma'aikatan kiwon lafiya a wurin bikin yaki da cutar zazzabin cizon sauro

Jihar Taraba ta bankado ma'akatan bogi dubu biyu yayin da take tantance ma'akatanta kafin to soma biyan sabon albashi
Rahotanni na cewa cikin wasu ma'aikata ya duri ruwa a jihar Taraba sabili da tantance ma'aikatanta kafin ta fara anfani da tsarin sabon albashi na nera dubu goma sha takwas a matsayin karamin albashi.

Sai dai yayin da aka soma tantancewar wasu mutane sun soma korafi, suna zargin an mayarda su saniyar ware. A cewarsu sai wadanda suke da daurin gindi ake shigar da sunanyensu cikin wadanda aka tantance.Sun ce kwamitin baya yi masu adalci domin ana nuna son kai.

Gwamnatin jihar ta ce dalilin tantancewar shi ne a bankado ma'aikatan bogi kafin a soma biyan sabon albashi kana kuma a kara daukan sabbin ma'aikata. Mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin kananan hukumomi da masarautu ya ce kwaliya ta soma biyan kudin sabulu domin tuni aka gano ma'aikatan bogi fiye da dubu uku. Ita ma kungiyar kwadago Najeriya reshen jihar ta goyi bayan tantancewar kuma zata sa ido domin kada a cuci ma'aikatan.

Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Taraba Ta Bankado Ma'aikatan Bogi - 3:10