Kamar gwamnatin tarayya, gwanatin jihar Nija ma tana ikirarin ta gano ma'aikatan bogi a jerin sunayen wadanda suke karbar albashi, cikin adadin ma'aikata sama da dubu 30 dake karkashinta.
Gwamnan Jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, wanda ya bayyana haka, yace gwamnati tana kashe fiye da Naira milyan dubu biyu wajen biyan albshi ako wani wata, amma aikin tantance ma'aikatan ya gano hanyoyin daban daban da ma'aikata suke bi na zalunci, kama daga saka sunayen wadanda basa aiki amma suna karbar albashi, da wadanda zasu sa a saka sunayensu a wasu ma'aikatu suna jan albashi da ya dara aikinsu da makamantansu.
Amma a nasa martanin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar,komored Yahya Idris Indako, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari, cewa, irin matsalolin da shirin tanatance ma'aikatan ya jefa ma'aikatan jihar ya isa haka. Daga yanzu zasu ja layi.
Kuma a shirye kungiyar take ta kai ruwa rana da gwamnatin jihar, idan tana zaton ko tsoronta suke yi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5