Sakamakon barkewar cutar nan mai suna Mas a kasar Saudiyya, gwamnatin jihar Neja a Najeriya ta yi fadakarwa ga mahajjatan don kare kansu.
WASHINGTON D.C —
Matakin da aka nuna musu su dauka a game da kare kan nasu shine, sun sami takunkumin baki don kare musayar numfashi.
Sannan mataki na biyu shine su tabbatar sun ci tsaftataccen abinci, musamman nama tare da tabbatar an dafa abincin da kyau.
An shirya wannan fadakarwa ne tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jihar Neja don tabbatar da ‘yan jihar ba su tafi kasar Saudiyyar da rashin sanin wannan cuta ba.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari daga Jihar Neja ya aiko mana da wannan rahoton cikin murya da ke kasa.
Your browser doesn’t support HTML5