JIHAR NEJA: Ruwan Sama Ya Kwashe Gidaje da Dama

Ambaliyar ruwa

Wani ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya ya kwashe gidaje da dama

Kimanin mutane dubu daya ne suka rasa muhallansu sanadiyar ruwan sama da isaka mai karfi da aka yi a garin Kuta.

Duk da yake ba'a samu asarar rai ba amma lamarin ya jefa jama'a cikin halin damuwa sakamakon asarar dukiya da suka yi.Mazauna garin sunn ce ruwan ya zo da isaka mai karfi wadda basu taba ganin irinta saboda haka gidaje da yawa suka bi ruwan.

Mutanen da abun ya shafa sun yi asarar komi da komi. Wasunsu basu fita da komi ba saboda ruwan ya yashesu kakaf. Hukomomin dake aikin bada agaji sun ziyarci garin Kuta to saidai mutanen garin suna rokon a yi masu taimako cikin gaggawa.

Dan asalin garin kuma dan majalisar wakilan Najeriya Onarebul Chika Adamu ya kai ziyarar jaje garin ya bada gudummawar nera miliyan daya tare da yi masu nasuha da su mayarda al'amarin ga Allah. Ya kira wadanda abun bai sameshi ba da su taimaka domin Allah ya tausaya masa ko da tasu zata zo wata rana nan gaba.

Gwamnan jihar ma Alhaji Abubakar Sani Bello shi ma ya ziyarci garin. Yace ya tausayawa wadanda iska ta kwashe gidajensu. Ya bada tabbacin gwamnati zata tallafa masu.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

JIHAR NEJA: Ruwan Sama Ya Kwashe Gidaje tare da Hallaka Mutane


.