Jami'an kiwon lafiya na jihar sun ce makon rigakafin cututtukan a kasashen Afirka yana da mahimmanci matuka idan aka yi la'akari da yadda cututtuka ke hallaka yara..
Cututtuka irin su bakon dauro da sankarau suna hallaka manya da yara. Dr Ibrahin Tifin babban sakatare a ma'aikatar kiwon lafiya ta Neja yayi karin haske. Yace idan kai kana da lafiya makwafcinka ka iya kamuwa da ciwo da ka iya yaduwa. Idan akwai rigakafi za'a samu sauki. Dalili ke nan da nahiyar Afirka tace a ware mako daya cikin watan Afirilu domin a fadakar da mutane akan mahimmancin yin rigakafi.
Hukumar lafiya ta duniya tana bukatar a samu raguwar mace mace sakamakon wasu cututtuka a kasashen Afirka. Dr Yabagi Aliyu daraktan matakin farko na ma'aikatar kiwon lafiya a jihar Neja yace burinsu ne akwai shirin rigakafi a kowane sakon jihar domin rigakafi ya fi magani. Da babu rigakafi da cututtuka sun yadu mutuwa kuma ta karu musamman mutuwar yara.
Ga Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5