Katse wutar lantarkin dai ya shafi ofishin samar da ruwansha a jihar.
Al’amarin da ya sa a yanzu haka ake fama da karancin ruwansha a kwaryar birnin Minna fadar Gwamnatin Jihar Nejan.
Kamfanin na AEDC dai ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda suna bin gwamnatin Jihar Nejan bashin Naira miliyan dubu daya da minayan 900.
Muhammad Adamu Pele shine jami'in hudda da jama'a na kamfanin mai kula da jihar Neja. Ya bayyan cewa umurni ne suka samu daga babban ofishin kamfanin dake Abuja.
Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce tana kokarin tattaunawa da kamfanin domin warware wannan matsala.
Sakataren Gwamnatin Jihar Nejan Alh. Ahmed Ibrahim Matane, ya ce duk da yake su ma sun sayama kamfanin na AEDC kayan aiki har na kimani naira miliyan dubu uku, amma bai hana su yin zaman sulhu da kamfanin ba.
Duk da jihar Nejan dai na da madatsun ruwa guda uku wato Shiroro, Kainji da kuma Jebba dake da tashoshin samar da lantarkin a Najeriya, amma kuma bayanai sun nuna cewa jihar na baya-baya wajen samun hasken lantarki a kasar.
Al’amarin da sakataren Gwamnatin Jihar Ahmed Ibrahim Matane ya ce abin takaici ne.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa akwai garuruwa da dama dake kewayen wadannan madatsun ruwa da kwata-kwata ma ba su da hasken lantarkin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5