A shekara ta 2013 ne gwamnatin jihar Kano ta fara aikin kafa tashar lantarki mallakarta a madatsar ruwa ta Tiga da ke yankin kudancin Kano a daidai lokacin da ma’aikatar lantarki da makamashi ta Gwamnatin tarayyar Najeriya ke aikin fadada tashoshin kula da samar da lantarki a jihohin Kano da Jigawa.
Tashar lantarkin wadda ke lakume biliyoyin naira, za ta rinka amfani da albarkatun ruwa daga Kogin Kano, kuma an tsara ta ne domin samar da makamashin lantarki ga masana’antu da kuma haskaka titunan birnin Kano da kewaye.
Alhaji Idris Garba Unguwar Rimi, kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Kano, ya ce aikin kafa tashar kashi biyu ne: janyo wutar da aka kusan kammala aikin da kuma dakon wutar zuwa inda za a rarrabata, shi ma ba don annobar COVID-19 ba da an kammala aikin, a cewarsa, amma ya suna sa ran nan da watanni 3 na farkon shekarar 2021 za a kammala aikin baki daya.
A hannu guda kuma, ma’aikatar makamashi da lantarki ta tarayya ta himmatu wajen habbaka na’urorin sarrafa lantarki da ke Jihohin Kano, Jigawa da kuma Katsina da nufin kyautata lantarki a jihohin uku.
Alhaji Sale Mamman, ministan lantarkin Najeriya, ya ziyarci daya daga cikin wuraren da aka kafa manyan na’urorin samar da lantarki a Kano ya kuma bayyana muhimmancin aikin.
Kwamishinan ayyuka na Kano ya nanata bukatar samar da karin irin wadannan injina da na’urori a jihar.
Duk da dimbin kanana da manyan masana’antu a Kano, jihar na kan gaba wajen fuskantar karancin lantarki a Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5