Jihar Jigawa ta Cika Shekara 23 da Kirkirota Daga Tsohuwar Jihar Kano

Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido

'Yan asalin jihar Jigawa basu nemi jihar ba domin ko an dannesu a tsohuwar Jihar Kano ne. Sun nemi jihar ne domin sun yi yawa a Kano kuma suna bukatar bunkasa cigaban al'umma.

Ranar 27 ga wannan watan jihar ta cika shekaru 23 da gwamnatin mulkin soja ta Janaral Ibrahim Babangida ta kirkirota daga tsohuwar jihar Kano.

Barrister Ali Sa'adu Birnin Kudu gwamnan farar hula na farko a Jigawa yace abubuwan da aka yi bayan ya sauka su ne abubuwan da dama zai yi da ya cigaba da mulki.

A wurin taron shagulgulan cika shekaru 23 da Jigawa ta zama jiha dukanin tsofofin gwamnonin jihar sun kasance in banda Sanata Saminu Turaki.

Aminu Ibrahim Ringim shugaban ma'aikatan gidan gwamnati dake Dutse yace yana zaton a shekara ta 1991 an yi jihohi sabbi guda shida ne. Cikin jihohin da aka kirkiro lokacin wacce jiha ce take biki cewa ta cika shekaru 23. Yace babu saidai jihar Jigawa. A jihar Jigawa kowane dan jihar an bashi tsaro yana zama lafiya.

Shugaban majalisar dokoki ta jihar Adamu Ahmed Sarawa cewa yayi lokacin da aka yi Jigawa ta hadu da abubuwa na rashin dadi amma daga lokacin da Sule Lamido ya kama mulki an samu gagarumin canji na cigaba.

Daya daga cikin matasa 'yan bokon Jigawa Barrister Kaloma Dahiru Mustapha yace yanzu ne Jigawa ta fara amsa takenta na sabuwar duniya. Yace sun fara gani kuma suna cikin farin ciki.

Tsohuwar ministar ilimi Farfasa Ahmed Rufa'i ta ja kunnen 'yan siyasar jihar musamman masu muradun neman kujerar gwamnan jihar. Duk wanda ya san ba zai kamanta ba kada ma ya nema. Ba zata yiwu jihar ta sake komawa baya ba. Yanzu kowa na alfahari da jihar. Wadanda basu san zasu zo arewa ba yanzu suna neman fili a jihar.

A shekarar 2008 gwamna Sule Lamido ya bullo da bikin murnar ranar zagayowar samun Jigawa a matsayin jiha. Gwamnan ya jagoranci bikin na bana. Yace taron ba na siyasa ba ne. Taron na duk 'yan asalin Jigawa ne. Tafiyar nan ta shekaru 23 an sha wuya amma Jigawa ikon Allah ce.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Jigawa ta Cika Shekara 23 da Kirkirota Daga Tsohuwar Jihar Kano - 3' 56"