Jihar Filato Ta Dauki Matakan Tabbatar Da Zaman Lafiya

Gwamnan Jihar Filato Barrister Simon Bako Lalong

Hukumar wanzar da zaman lafiya ta jihar Filato ta yi binciken dalilan yawan tashin hankali a jihar tare da yin nazari sannan ta fitar da wani shiri na shekara biyar domin tabbatar da zaman lafiyan

Daraktan hukumar dake inganta zaman lafiya a jihar Filato Mr. Joseph Lengman ya ce bayan rigingimun shekarun baya da wadanda jihar ta fuskanta cikin 'yan kwanakin nan suka ga yakamata su fito da wani tsarin zaman lafiya ta hanyar gano musabbabin haddasa ricin.

A cewar Mr. Lengman yakamata a samu wani shiri na musamman a gano dalilan da suke haddasa tashin hankali a jihar da yanzu ya kwashe shekaru goma zuwa goma sha biyar ana fama dashi. A gano matsalolin da wadanda suke harzuka mutane su tayar da hutsuma.

Injishi sun zauna da kungiyoyi daban daban sun yi bincike tare da yin nazari sannan suka fitar da tsari na shekara biyar. Ya bukaci mutane su goyi bayan shirin su kuma yi aiki dashi. Bayan shekaru biyar sai kuma su yi waiwaya su ga abun da suka yi. Idan kuma akwai gyaran da zasu yi sai su yi.

A makon jiya ne gwamnatin Filato ta ayyana dokar takaita zirga zirga a karamar hukumar Bassa bayan yamutsin da ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi da dama.

Shugaban raya kabilar Irigwe Mr. Sunday Abdu ya ce duk da dokar takaita zirga zirgan har yanzu ana kai hari kan al'ummar. Injishi sun zauna da Fulani da sarkin Irigwe sun ba Fulani hakuri a zauna lafiya. Sun kafa kwamitin da ya kunshi kabilun biyu kuma sun yi yarjejeniya. Hausawan garin Miyango da Kwal sun yadda sun sa hannu. Kabilar Irigwe ta sa hannu amma Fulani sun ki.

Amma shugaban kungiyar Fulani reshen karamar hukumar Bassa Umar Bakari ya ce yin adalci ga kowane bangare ne kadai zai tabbatar da zaman lafiya a yankin. Ya ce ba da Fulanin yankin suke fada ba amma kuma 'yan Irigwe sai su kai magana Abuja a zo ana kama masu matasansu.

Yanzu dai karamar hukumar Bassa ta kafa kwamiti mai mutane 21 da zai binciki musabbabin rikicin.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Filato Ta Dauki Matakan Tabbatar Da Zaman Lafiya - 4' 28