A shirin da jihar Borno keyi na mayar da 'yan gudun hijira garuruwansu, yanzu gwamnati ta fara sake gina garuruwa da wuraren more rayuwa da asibitoci har ma da ofisoshin 'yansanda a kananan hukumomi 20 da 'yan Boko Haram suka yi raga-raga dasu.
Gwamnatin ta raba gine-ginen kashi kashi saboda yadda take samun kudin shiga. Yanzu dai gwamnatin ta soma da kananan hukumomi guda biyar daga bisani kuma a fadada zuwa wasu.
An kusa gama aikin karamar hukumar Kaga har ma gwamnan jihar ya ziyarci wurin domin gani da ido.
Gwamnan yace da yaddar Allah nan da zuwa karshen wata mai zuwa zasu kammala aikin kana mutanen wurin dake gudun hijira su samu su koma garuruwansu. Gine-ginen sun hada da gidajen kwana da asibiti da makaranta da masallatai da barikokin 'yansanda. A wani wurin ma har an gama aikin ruwan sha kamar Jakana.
Gwamnati ta tara nera miliyan dari bakwai. Idan kudin ya kai biliyan daya zasu fara kashi na biyu.
Dangane da sake gina Baga gwamnan yace suna sa ran shugaban kasa zai amince da bada tallafin gina karamar hukumar da garin.
Alhaji Babagana Umara kwamishana na musamman akan sake gine-ginen garuruwan yace sun fara da kananan hukumomi hudu ssuna kan na biyar haka zasu dinga cigaba da aikin da zara sun sami kudi.
Mazauna garuruwan da ake kan sake ginasu sun yi murna tare da godiya.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5