Barcelona da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal sun jera sahu guda wajen zawarcin dan wasan baya na RB Leipzig, dan shekara 21 da haihuwa, wanda yake buga wa 'yan kasa da shekara 21 a kasar Faransa, mai suna Dayot Upamecano.
Kungiyar ta Barcelona ta ce tana neman dan wasan ne domin ya maye mata gurbin dan wasanta Samuel Umtiti, wanda Manchester United take shin-shinar sa da ya koma gareta.
Ita kuwa kungiyar Arsenal tana bukatar sayen dan wasan na RB Leipzig ne domin ta cike gurbin dan wasanta Calum Chambers, wanda yake fama da jinyar da zata hanashi buga wasa har karshen kakar wasan bana.
A kan haka ne suke gwagwar maya da Barcelona kan sayen dan wasan Upamecano inda aka masa darajar kudi fam miliyon £45.
Sai dai Barcelona zata fi bada karfi ne kan sayen Umtiti da Manchester take so kafin karshen watan Janairun bana da za'a rufe hada hadar saye na 'yan wasa.