Jawabin Sarkin Kano A Yayin Bukukuwan Sallah A Birnin Kano

Miliyoyin al’umar musulmi ne suka yi sallah a masallatan Idi daban daban a birnin da kewayen jihar Kano.

Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi, na biyu ya nanata muhimmancin kaunar juna tsakanin musulmi. Mata da maza da yara kanana ne su ka yi dandazo a masallatan Idi daban daban fiye da dari a sassan birnin Kano da kewaye.

A jawabinsa na Sallah, mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi Na biyu, ya ja hankalin al’umma akan muhimmancin zumunci da kaunar juna, kana ya bukaci al’umma suyi katin zabe da kuma mallakar katin zama dan kasa.

Dr Muhammad Sani Ayagi, limamamin daya jagoranci sallar Idi a fillin Idi na harabar tsohuwar Jami’ar Bayero a kano a cikin hudubar da ya gabatar kafin fara sallar idin ya tabo tarihin sallar layya kwana daya bayan tsayuwar Arfa.

Ya tabo Batun hadin kai tsakanin musulmi inda ya ce hadin kai shine batun da ya mamaye hudubar galibin limaman da suka gabatar da huduba a yau, shi-ma Dr Muhammad Sani Ayagi, ya yi tsokaci game da haka, ya ja hankalin ‘yan siyasa game da zabuka masu zuwa.

A sakon sa na Salla, Gwamman Kano ya nanata aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da wanzar da zaman lafiya domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar Jama’ar Kano.

Your browser doesn’t support HTML5

Jawabin Sarkin Kano A Yayin Bukukuwan Sallah A Birnin Kano 3 '39"