Jarumi Adam Zango Ya Dauki Nauyin Dalibai 101 A Birnin Zariya

Adam A Zango

A jiya ne jarumi Adam Abdullahi Zango ya bada tallafin karatu ga dalibai 101, a makarantar da ake kira da sunan Farfesa Ango Abdullahi International School, a matsayin gudunmawa wajen yi wa kasa hidima.

Ya ce babban dalilin da ya sa ya bada wannan tallafin, shine ganin yadda matsaloli ilimi a yankin Arewa suka ta'azzara.

A hirar su da wakiliyar muryar Amurka Baraka Bashir, Adam ya shaida mata cewar wannan ba shi ne karo na farko da ya fara bada tallafi ba, domin da farko yakan bada tallafi kamar zuwa yara uku, ko goma, har Allah ya sa yanzu ya kai ga bada tallafin ga dalibai 101. Ya kara da cewar yayi hakan ne a matsayin sadakatul jariya.

Kowa ya sani cewar, ana da matsalar almajiranci a arewa, kuma ana ta cece-kuce, ana jiran gwamnati tayi wani abu akai, alhali akwai jama'a da zasu iya taimakawa. Shi yasa a matsayinsa na dan kasa ya dora dammara, ya bada tasa gudunmuwar ga kasar sa, da kuma al'ummarsa 'yan Arewa.

A nasa bangaren Firincifal Malam Hamza Jibril ya ce wannan wani babban abu ne, kuma tabbas wannan jarumin ya bada wannan tallafi ne domin marayu da suke zaune a birnin Zariya dake jihar Kaduna.