A yau Jumma’a majalisar dokokin Japan ta zartas da kudurin dokar da zata kyale Sarkin Sarakuna na kasar Akihito, ya sauka daga kan kujerarsa, a mika wa babban dansa, Yarima mai jiran gado Naruhito mai shekaru 57 da haihuwa.
Sarki Akihito dan shekaru 83, wanda aka yiwa tiyatar Zuciya kuma aka yi masa maganin ciwon daji a kakar bara, ya nuna bukatarsa ta yin murabus bayan rike mulkin na kusan shekaru 30, hakan ya tayar da tsohuwar muhawara a Japan akan matsalar gado a masarautar mai tsohon tarihi na shekaru kusan 2,000 .
Wannan murabus dai zai zamo na farko tun shekaru 200 da suka gabata. Akihito ya hau kan karagar mulki yana dan shekaru 56 a watan Janairu na shekarar 1989 bayan rasuwar mahaifinsa, Sarki Hirohito.
Kafafen yada labarai na bada rahotannin cewar Jami’ai na jiran shekarar 2018, yayin da Akihito zai cika shekaru 85 kafin yin murabus din.
A kuri’ar da aka kada wacce aka nuna ta kai tsaye a gidan Talabijin na NHK, yan majalisa a babbar majalisar sun aiwatar da dokar a yau Juma’a bayan karamar majalisa ta bada izinin dokar satin da ya gabata.
Yin Murabus din za’ayi shine cikin shekaru uku daga lokacin da aka kafa dokar ko kuma ta lalace, kuma zatayi aiki ne kadai akan Akihoto.
Sarkin Japan da ya taba yin murabus a tarihin kasar shi ne Kokaku a shekarar 1817.