Prime Ministan Japan Ya Yiwa Amurka Ta’aziyar Shekaru Saba’in

Prime Ministan Japan Shinzo Abe ya nuna alhini a lokacin da ya yiwa Amurka ta’aziyar mutuwar fiye da Amerikawa dubu maitan da dari hudu a lokacin da kasar sa ta kaiwa Peral Harbour a Hawaii hari shekaru saba’in da biyar da suka shige.

Wannan harin ba zata da Japan ta kawo a ranar bakwai ga watan Disamban alif dari tara da arba’in da daya ya zama sanadin da Amirka ta shiga yakin duniya na biyu.

Prime Ministan na Japan ya fada a jiya Talata cewa kada mu sake maimata irin wannan razana ta yaki.

Yace a matsayinsa na Prime Ministan Japan ina yiwa Amirka ta’aziyar wadanda suka mutu.

Shi dai Mr Abe bai nemi gafarar harin da kasar sa ta kai Pearl Harbor ba. Prime Ministan ya tsaya kusa da shugaba Barack Obama na Amirka a lokacin wani biki da

aka yi a wani sansanin hadin gwiwa dake birnin Honolulu jihar Hawaii a jiya Talata