Janyewar Najeriya Daga Yarjejeniyar Kasuwanci Ta Nahiyar Afirka Ya Bada Mamaki

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari wanda ya janye daga yarjejeniyar

A ganin Farfesa Murtala Sabo Sagagi janyewar da Najeriya ta yi daga yarjejeniyar kasuwanci na kasashen Afirka da suka kawashi shekaru uku suna kai komo a kai har sai da dukanasu suka amince, ba wani abu ba ne rashin shiryawa ne

Masana harkokin tattalin arziki a Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayi dangane da matakin da gwamnatin kasar ta dauka a jiya na kin sanya hannu akan yarjejeniyar habaka harkokin kasuwanci da masana’antu a tsakanin kasashen Afrika.

A zantawa da wakilin Muryar Amurka a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya yi, shugaban tsangayar nazarin harkokin kasuwanci da tattalin arziki ta Dangote dake Jami’ar Bayero, Kano, Farfesa Murtala Sabo Sagagi, ya ce matakin na Najeriya abun kunya ne, la’akari da matsayin ta na Jagora a nahiyar Afrika. Sai dai Farfesa Murtala Sagagi ya fara ne da fayyace abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa.

A cewarsa yarjejeniyar ta kunshi wasu kudurori da aka cimma tsakanin kasashen Afirkan 55 domin saukaka kasuwanci da bangaren masana'antun Afirka saboda ana fada cewa kasashen Afirka basa kasuwanci tsakaninsu sai da kasashen Turai, Amurka ko kasashen Asiya. Ana ganin idan aka yi yarjejeniya za'a rage haraji da ake biya akan kayan masana'antu.

A cikin 2012 aka yarda za'a yi yarjejeniyar amma an yi shakaru uku ana tattaunawa domin kawo daidaito. Najeriya na kan gaba a cikin kasashen da suka tattauna yarjejeniyar.

A cewar Farfesa Sagagi Najeriya ta janye ne domin bata shirya ba ne amma yawancin kasashen sun shirya. Akwai bangarorin Najeriya da dama da basu san ma abun da ake shiryawa ba. Injishi abun kunya ne a ce Najeriya ta janye.

Saidai Farfesa Sagagi na ganin yarjejeniyar ba zata yi tasiri ba idan babu Najeriya ciki.

Ga rahoton Ibrahim Kwari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Janyewar Najeriya Daga Yarjejeniyar Kasuwanci Ta Nahiyar Afirka Ya Bada Mamaki -4' 28"