Wakiliyar Muryar Amurka ta fara da tuna mashi cewa wannan karon shi ne zai zama na hudu da Janaral din zai tsaya takarar neman zama shugaban Najeriya.
Dangane da ko yana da karfin gwiwar cin zaben shekara mai zuwa a wannan karon Janaral Buhari yace yana da karfin gwiwa saboda duk zabuka ukun ya dauki kara dasuka kai har kotun koli. Daga kotun koli a cikin tsarin Najeriya sai dai mutum yayi Allah ya isa.
Duk zabukan da aka yi a shekarar 2003, 2007 da 2011 yace sun tara hujjoji wadanda akan doka yakamata a ce yaci zabe saboda kundun tsarin mulkin 1999 ya kafa tsarin yadda za'a yi zaben. Daya daga cikin aikin hukumar zabe ita ce ta kafa jam'iyyu. Duk wanda yake son a zabeshi kowane mukami kama daga kansila zuwa shugaban kasa dole ya bi ta jam'iyya.
Kafin kowane zabe sai an yi dokarsa. Yanzu suna jiran dokar 2014 akan zaben 2015. Saboda haka a rubuce a takarda ba'a iya kama Najeriya. Sai dai kurum a sa a kwandon mantuwa a ki anfani dashi. A kundun tsarin milkin Najeriya an ce mutum ba zai jefa kuri'a ba sai ya kai shekara 18. Amma ba'a ce ko ka shekara dari da zaka iya tsayawa takara ba. Saboda haka domin yayi sau uku zai kuma yi na hudu yana cikin garalinsa, wato ganin damarsa yayi. Kuma yana da niyar yin takararar. Sabili da haka zai gayawa jama'a zai yi kuma zai nemi jam'iyyarsa ta sake tsayar da shi.
Janaral Buhari ya musanta batun cewa yayi murabus daga siyasa. Sai dai yace ba zai sake bada sunansa ba domin ya nemi takara. A wannan karon mutane daga jihohi daban daban sun zo sun sameshi cewa yunda bai bar siyasa ba yakamata ya tsaya.
Ga rahoton Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5