“Anyi adalci idan ka lura da abunda aka yi, domin an baiwa kowani dan takara dama ya bayyana abunda yake son yi, da yadda ya fahimci matsalolin kasarnan (Najeriya), da kuma abunda zaiyi idan ya samu shugabanci”, a cewar gwamnan na Sokoto.
Mr. Wammako ya cigaba da cewa “duk wanda ya san gaskiya, ya san cewa wannan zaben da aka yi, to akwai taimakon Allah a ciki, amma irin sanin da akayi wa Janar, mutane sun san cewa zai iya kawo canjin da ake bukata cikin yardar Allah.”
Gwamna Wammako yayi karin haske game da irin salon shugabanci da dan takarar Janar Buhari ya sani, da kuma abunda zai fuskanta a demokradiyyanci idan yayi nasara.
“Mulkin da yayi can da, na soja ne. Muka zo yanzu na siyasa ne, akwai ban-banci tsakanin mulkin soja da na siyasa. Mu da muka zabe shi, dole mu bashi goyon baya don ya samu nasara.”
Your browser doesn’t support HTML5