Janar Ibrahim Babangida Yayi Barazanar Ficewa Daga Jam'iyyar PDP

Janar Ibrahim Babangida mai ritaya

Tsohon shugaban yace kulle-kullen da ake yi ka'in da na'in na tsayar da shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP ya keta dokokin jam'iyyar.

Tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida yayi barazanar cewa zai bar jam’iyyar PDP mai mulkin kasar, a saboda cacar-bakin da ta kaure a kan ko daga wani bangare ya kamata jam’iyyar ta fito da dan takarar shugaban kasarta a shekara mai zuwa.

A cikin wata wasikar da ya rubuta ranar talata, Janar Babangida yace tsayar da shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP ya keta dokokin jam’iyyar. Jam’iyyar, wadda dukkan mutanen biyu suke membobinta, tana da manufa ta karba-karba a tsakanin Musulmi daga arewa da kuma Kirista daga kudu a bayan kowane wa’adi biyu na shugaban kasa.

Babangida ya ce zai sake nazarin ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar ta PDP a saboda yadda ake ci gaba da keta tsarin mulkinta.

A watan da ya shige, wani kwamiti na dattijan arewa masu fada a ji, yace zai goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, domin ya kalubalanci Mr. Jonathan a zaben fitar da dan takara na jam’iyyar.

Najeriya tana shirin gudanar da zaben ‘yan majalisun dokoki ranar 2 ga watan Afrilu, da kuma zaben shugaban kasa a ranar 9 ga watan.