Yanzu sojojin sun kirkiro wani dan karamin jirgin leken asiri wanda zai dinga zakulo 'yan Boko Haram a koina suke da buya a duk fadin arewa maso gabashin Najeriya.
Babban Hafsan Hafsoshin sojojin Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai yace dama can sun fada cewa za'a cigaba da samun hare-hare jifa-jifa amma yin hakan bai nuna cewa ba'a fi karfin 'yan ta'adan ba.
Janar Buratai yace yanayin yadda kasar take yana taimaka ma 'yan ta'adan saboda akwai hanyoyin dama da suke da wuyar shiga. Fasahar da suke da ita zata taimaka masu su san inda 'yan ta'adan suke a koina su zakulosu.
Janar Buratai yayi bayanin yadda jiragen zasu takarawa dangane da zakulo 'yan Boko Haram daga wuraren buyansu. Suna da jirgin dake iya leken nesa a san abun da yake faruwa. Duk 'yan ta'ada da masu mugun nufi za'a iya ganosu.
Air Commodor Ahmed Tijjani Baba Gamawa masani kan harkokin tsaro. Yace dabarun da sojojin suka fito dasu na zamani su suka fidacewa. Jirgin zai gano masu dauke da makamai zai kuma banbance mutum da dabbobi.
Dangane da abun da yakamata a yi ganin yadda 'yan Boko Haram ke cigaba da kai hare-hare, Aliko Harun tsohon hafsan leken asirin sojojin Najeriya yace akwai abubuwa ukku da yakamata a yi. Na daya yace yakamata a kawo karshen goyon bayan da 'yan Boko Haram suke dashi cikin jama'a wadanda suke mara masu baya. A zakulosu. Na biyu shin akwai wadanda suke cin riba da yakin walau sojoji ko 'yan siyasa? Yace ba za'a rasa su ba. Na ukku a karfafa tattara bayanan siri akan 'yan Boko Haram.
Ga rahoton Hasan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5