Janar Abdulsalam Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Kai Zuciya Nesa

Taron da shugabannin Najeriya suka yi domin tabbatar da zaman lafiya a zaben 2019 a Abuja

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalamu Abubakar, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kai zuciya nesa bayan dage babban zaben kasar da hukumar INEC ta yi.

Abdulsalam ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya yi bayan ka-ce-na-ce da ake ta yi dangane da matakin hukumar zaben ta INEC ta dauki na dage zaben zuwa 23 ga watan Fabrairu.

Janar Abdulsalamu Abubakar din wanda shine shugaban wata kungiyar zaman lafiya, yace duk da yake yasan akwai kace nace akan dalilin daga wannan zaben sudai bukatar su shine a zauna lafiya.

“Tun da aka canza wannan zabe zuwa ranar Asabar ta makon gobe, ina rokon ‘yan uwana don Allah don Annabi a yi hakuri a zauna lafiya, kada a tada hakali. Na san akwai takaici, mutane sun yi tafiye – tafiye, sun je inda za su kada kuri’arsu, amma awa biyar kafin ayi zabe, aka daga wannan zaben, wannan akwai takaici, saboda haka muke rokon jama’a mu yi hakuri”. Inji Abdulsalam, wanda shi ne shugaabn wata kungiyar wanzar da zaman lafiya.

A daren ranar Juma’a hukumar zaben ta Najeriya INEC ta dage zaben bisa dalilai masu nasaba da tangardar da aka samu wajen raba kayayyakin aiki da wasu jihohi ba su samu ba.

Har ila yau, Janar Abdulsalamu Abubakar ya bukaci kafofin yada labarai da su rinka tantace labaran da suke yada wa, domin kaucewa haddasa rudani a tsakanin jama’a.

Daga bisani Janar Abdulsalamu Abubakar ya ce kungiyarsu ta taimaka wajen tsabtace yakin neman zabe a tsakanin ‘yan siyasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Janar Abdulsalam Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Kai Zuciya Nesa 03'01"