Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta kasar Jamus tare da hadin gwuiwar gidan rediyon Jamus da na Unity FM dake Jos sun gudanar da taron fadakarwa kan yawan hadarin da 'yan Afirka masu kokarin ketarawa kasahen turai ta barauniyar hanya ke fadawa.
Taron mai taken 'Hangen Dala ba shiga birni ba" ya tattaro kwararru da suka tattauna a kan dalilan dake sanya matasa barin kasarsu zuwa turai ta kowace hanya da kuma zakulo hanyoyin da za'a samu masalaha.
Alkalumma na nuni da cewa matasa fiye da dubu goma ne daga Najeriya suka tsallaka kasashen turai cikin wannan shekara ta 2017.
A cewar wani mai fafutikar kwato 'yancin 'yan Adam Dr. Aliyu Tilde akasarin masu tafiya turai ta barauniyar hanya suna gujewa matsaloli ne daga kasashensu. Yana mai cewa mutane na fita zuwa turai saboda ana ganin kasashe ne masu kwatanta adalci da tsare gaskiya da 'yanci. Suna gujewa abubuwa kamar wariya saboda addini ko yaki ko yunwa ko kuma kabilanci.
Ita ma Madam Jummai Madaki jami'a dake aiki da kungiyar dake yaki da fataucin mata da yara ta ce akwai masu yaudarar yara mata suna kaisu turai ta barauniyar hanya da sunan samar masu ayyukan yi.
Hajiya Hadiza Gambo Hawaja tace rashin ba matasa ayyukan yi na janyo kaura da suke yi zuwa kasashen ketare.
Shugaban Sashen Hausa na gidan rediyon Jamus ya ce sun shirya taron ne domin illimantar da jama'a. Yana mai cewa a can turai matsalar bakin haure matsala ce da take ci masu tuwo a kwarya. A nan Afirka kuma matasa na son zuwa turai ta hanyar dake da mugun hadari shi ya sa "suka ga ya kamata su ilimantar dasu".
Shi ma ministan matasa da wasanni Barrister Solomon Dalung yace gwamnati na iyakar kokarinta wajen tallafawa matasa. Yana mai cewa a shekarar 2016 gwamnatin tarayya ta ware N500bn domin taimakawa matasa. Ta dauki matasa 200,000 aiki tana biyan kowannensu N30,000 ko wane wata.
Shi ko shugaban gidan rediyon Unity FM kuma tsohon ministan sadarwa Ibrahim Salihu Dasuki Nakande ya ce zasu cigaba da fadakar da al'umma. Iyaye zasu ji zasu kuma fahimta koda ma wani barawon yara zai zo ya yi kokarin yaudararsu.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5