Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya mika hannun sulsu jiya Asabar ga Turawan kasar, sannan ya ce ba za a kara mamaye masu gonaki ba.
A wani matakin da ya saba da salon jam’iyyarsa ta ZANU-PF mai mulki, wadda kan dauki Turawan a matsayin baki tare kuma da kwace masu gonaki a karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Robert Mugabe, Shugaba Emmerson Mnangagwa ya yi kira ga Turawan da su kada masa kuri’a a babban zaben kasar Zimbabwe da za a yi ranar 30 ga watan Yuli, ya na mai masu alkawarin samar masu da kasar noma.
Mnangagwa na jawabi ne a taron da ‘yan jam’iyyarsu ta ZANU-PF ke kira “Gangamin zawarcin Farar fata,” wanda aka shirya da zummar samun kuri’un Turawa, wadanda mutumin da Mnangagwa ya gada, wato Mugabe, ya kan ce, “matattunsu ne kadai ke da amfani.”