Shugaba Obama yana magana ne a wajen kamfe da yake yiwa ‘yar takarar jamiyyar Democrat Hillary Clinton a Jihar North Carolina wadda take jiha ce da take da dimbin tasiri ga ‘yan takara, domin ko tilas neko wane dan takarar dake son shiga fadar White House to wajibi ne yayi nasara a wannan jihar.
Shugaba Obama yaci gaba da cewa bai jin cewa Amurka na cikin hatsari da ace ya fadi zabe lokacin da ya kara da John Mccain a shekarar 2008 ko kuma Mit Romny a shekarar 2012.
A dai dai nan ne yake gargadin masu jefa kuri’a na jihar ta North Corolina da cewa kar su dauka cewa kuri’ar ko wane mutum guda bata da tasiri. Yace sam wannan zaben ya wuce da haka, don haka kar su shantake gida suki zuwa jefa kuria domin yin hakan wata babbar illa ce ga wakilcinsu.
Shugaban yana magana ne musammam ga masu jefa kuri’a bakaken fata, wadandabasu nuna sha’awarsu ba domin kurun shi Obama baya takara wannan karon.
Sai dai kuri’ar baya-bayan nan a jihar ta North Carolina ta nuna cewa Trump na gaban Hillary da ‘yar tazara kadan wanda bai taka kara ya karya ba.
Shiko Trump a lokacin da yake yakin neman zabensa a jihar Florida yace zaben Clinton zai haifar da mummunar matsala ga dokar kasa wanda za’a dade ba a shawo kansa ba. Yace yadda ta sarrafa Email lokacin da take sakatariyar harkokin wajen kasar zai jefa ta cikin bincike koda ko tana shugabanci.