JAMI’IYYAR PDP TA BUKACI A GAGGAUTA SAKO MATA KAKAKIN TA.

  • Ladan Ayawa

PDP

Cikin sanarwan dake dauke da sakataren jamiyyar na Kasa Farfesa Adewole Oladipo jamiyyar ta PDP ta bukuci hukumar EFCC ta gaggauta sako mata kakakin ta Mr Oliseh Metuh da ake zargi da halarta kudin haram sama da naira miliya dubu.

Jamiyyar ta PDP tace kame Oliseh Metuh bai zo mata da mamaki ba idan akayi la’akari da barazanar da aka ce yasha huskanta daga jamniyyar APC dama gwamnatin tarayya wadda tace ta shiga rudani kuma take kokarin rufe bakin ‘yan adawa.

Sai dai da wakilin Muryar Amurka ya tuntubi mataimakin kakakin jam’iyyar na kasa Barister Abdullahi Jalo kan wannan kame , ga kuma abinda yake cewa.

‘’PDP tasha fadin cewa tana goyon bayan hana cin hanci a Najeriya, shin a Oliseh Metuh gayyatar sa da aka yi abinda yakamata kowa ya sani cewan idan an kama mutum cewa akayi akai shi kotu kada ya wuce awa 24.Ai babu wanda zaice maka an same shi da laifi kotu ce take da wannan hurumin mu jira muji kotu me zata yi, EFCC ai ba kotu bace haka kuma maganganun cikin gari ba kotu bane’’

Sai dai da aka tambayi Barister cewa sakataren jamiyyar tasu yace kame Oliseh Metu bita da kulli ne?.

Anan ko sai yace bai yiyuwa Sakatare na magana shi ma yana Magana.

Ga dai Hassan Maina Kaina da Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

JAMI’IYYAR PDP TA BUKACI A GAGGAUTA SAKO MATA KAKAKIN TA. 1'51